Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Pompeo da firaministan Sudan sun tattauna batun tsame Sudan daga jerin kasashen dake daukar nauyin ta'addanci
2020-10-23 13:53:36        cri

A jiya Alhamis sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya tattauna ta wayar tarho da firaministan Sudan Abdalla Hamdok, game da batun fitar da kasar Sudan daga cikin jerin kasashen dake daukar nauyin ayyukan ta'addanci, da kuma batun dangantakar Sudan da Isra'ila.

Sakatare Pompeo, da firaminista Hamdok, sun yi maraba da matakin da shugaban Amurka Donald Trump, ya dauka na cire kasar ta Sudan daga cikin jerin kasashen dake daukar nauyin ta'addanci, wannan wani muhimmin mataki ne game da alakar dake tsakanin kasashen biyu, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta bayyana.

Sanarwar ta kara da cewa, bangarorin biyu sun bayyana muhimmancin gaggauta amincewa da dokar zaman lafiya wanda majalisar wakilan Amurka ta amince da ita.

Pompeo, ya yabawa Hamdok, a kokarinsa na kyautata dangantakar dake tsakanin Sudan din da Isra'ila, kuma ya jaddada kyakkyawan fatan lamarin zai cigaba da gudana.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China