Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka za ta cire Sudan daga jerin kasashen dake daukar nauyin ayyukan ta'addanci
2020-10-20 09:25:56        cri
Shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar jiya Litinin cewa, zai cire sunan kasar Sudan daga jerin sunayen kasashen dake daukar ayyukan ta'addanci, bayan Sudan din ta biya Amurkawan da ayyukan ta'addanci ya shafa dala miliyan 335.

Trump ya wallafa a shafinsa na Tiwita cewa,"labari mai kyau, sabuwar gwamnatin Sudan wadda ke samun ci gaba, ta amince ta biya iyalai da daidaikun Amurkawa da ayyukan ta'addanci suka shafa, dala miliyan 335. Kuma da zarar sun saka wadannan kudade,za a cire sunan kasar ta Sudan daga jerin sunayen kasashen dake daukar nauyin ayyukan ta'addanci. A karshe an yiwa Amurka adalci, kuma wannan babban ci gaba ne ga bangaren Sudan".

Rahotanni na cewa, cire sunan kasar Sudan daga jerin sunayen, zai taimaka wajen daidaita alaka tsakanin Sudan da Isra'ila, matakin da Trump zai dauka a matsayin karin nasara ga manufofin harkokin wajen Amurka, yayin da ake kasa da makonni uku kafin zaben shugabancin kasar ta Amurka.

A watan Agusta ne, firaministan kasar Sudan Abdalla Hamdok, ya bukaci gwamnatin Amurka, da ta bambance tsakanin shirin cire sunan kasar daga jerin sunayen kasashe da Amurka ke dauka a matsayin masu daukar nauyin ayyukan ta'addanci da kuma batun daidaita alaka da Isra'ila.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China