2020-10-22 11:05:03 cri |
Gwamnatin Birtaniya ta sanar a jiya Laraba cewa, za ta koma kan teburin tattaunawar inganta makomar alakar dake tsakaninta da kungiyar tarayyar Turai EU a cikin wannan mako a birnin Landan, kwanaki kadan bayan da ta ayyana cewa an kammala cimma daidaito na bayan ficewa kasar daga tarayyar Turai.
A sanar da gwamnatin Birtaniya ta fitar, ta ce, a shirye suke su karbi bakuncin tawagar EU zuwa birnin Landan domin dawowa kan teburin tattaunawar a cikin wannan mako. Sanarwar ta ce sun riga sun kammala tsara dukkan ka'idojin da suka dace bisa hadin gwiwa domin shiga muhimmin zagayen tattaunawar.
Zagayen farko na tattaunawar zai gudana ne a Landan daga ranar 22 zuwa 25 ga watan Oktoba.
Ta kara da cewa, a bayyane take cewa, akwai muhimmin gibi da ya rage game da matsayar kasar Birtaniya a bangarori masu wahalar gaske, amma a shirye suke, tare da EU, domin duba yiwuwar cike wadannan gibin a lokacin muhimmiyar tattaunawar.
Haka zalika, kakakin gwamnatin Birtaniya ya ce, an samu gagarumin ci gaba ta hanyar kalaman da babban mai shiga tsakani na EU Michel Barnier, ya bayyana a taron majalisar EU na ranar Laraba cewa, dukkan bangarorin biyu a shirye suke su yi hadin gwiwa da juna.
Sai dai kuma, Birtaniya ta yi gargadin cewa, har yanzu ba a tabbatar da daddale yarjejeniyar kasuwanci tsakanin sassan biyu ba.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China