Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jimillar mutanen da aka yiwa allurar rigakarin COVID-19 ta Sin ta kai dubu 60
2020-10-21 11:14:09        cri

Mataimakin shugaban hukumar kimiyya da fasahar raya zaman takewar al'umma ta ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Tian Baoguo ya bayyana a taron manema labarai kan aikin rigakafi da kuma dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19 da majalisar gudanarwar kasar Sin ta kira a jiya Talata cewa, ana gudanar da gwajin allurar guda hudu kan mutane bisa mataki na uku lami lafiya, kuma ga alamu, allurar ba su wata illa ga lafiya.

Kana shugaban rukunin SINOPHARM wato rukunin maganin kasar Sin Liu Jingzhen ya bayyana cewa, ana yin gwajin allurar rigakafin cutar COVID-19 guda biyu da cibiyar nazarin halittu ta birnin Beijing da cibiyar nazarin halittu ta birnin Wuhan suka samar a kan mutane a kasashe goma dake hada Hadaddiyar Daular Larabawa da Jordan da Peru da Agentina da Masar da sauransu bisa mataki na uku, kawo yanzu jimillar mutanen da aka yiwa allurar ta kai wajen dubu 50, kawo yanzu allurar ba su wata illa ga lafiya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China