Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin watsa labaran Birtaniya da Amurka sun yabawa shigar Sin cikin shirin COVAX
2020-10-11 16:33:08        cri

Labarin da aka gabatar a shafin yanar gizo na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin a ranar 8 ga wata ya nuna cewa, kasar Sin ta kulla yarjejeniya da kungiyar samar da allurar rigakafin cututtuka ta kasa da kasa, domin shiga shirin samar da allurar rigakafin COVID-19 wato COVAX a hukumance.

A jiya, babban darektan hukumar kiwon lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi nuni da cewa, ba zai yiwu a samar da isasshen allurar rigakafin cutar COVID-19 bisa mataki na farko ba, amma idan aka raba allurar bisa adalci, wato kasashen duniya wadanda suka shiga shirin allurar rigakafin COVID-19 su samar da allurar ga mutanen da suka fi bukata tare, misali ma'aikatan kiwon lafiya da tsoffafi da mutanen da suke fama da cututtuka iri daban daban, an kimmanta cewa, adadin allurar rigakafin cutar da za a samar zai kai biliyan 2 kafin karshen shekarar 2121.

Kana kasar Sin ta shiga shirin a hukumance, lamarin da ya jawo hankalin kafofin watsa labaran kasa da kasa matuka.

Jaridar The Guardian ta Birtaniya ta ba da labari cewa, shirin allurar rigakafin COVID-19 zai tabbatar da cewa, wasu mutane na daukacin kasashen duniya za su samu allurar, a maimakon daukacin mutanen wasu kasashe, yanzu haka kasar Sin ta shiga shirin, lamarin da ya kara karfafa imanin al'ummun kasa da kasa yayin da suke kokarin kandagarkin annobar, ana iya cewa, lamarin ya kara kyautata kimar kasar Sin a idon al'ummun kasa da kasa, saboda lamarin ya nuna cewa, kasar Sin tana yin adawa da ra'ayin nuna fifiko kan al'ummun kasashe daban daban, yayin da ake raba allurar rigakafin annobar, bisa matsayinta na kasa mafi girma dake cikin kasashen da suka daddale yarjejeniyar shiga shirin.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters na Birtaniya shi ma yana ganin cewa, shigar kasar Sin cikin shirin zai inganta ci gaban shirin, saboda shirin zai hana wasu gwamnatocin kasashe su adana allurar rigakafin, don haka za a samar da allurar ga wadanda suka fi bukata a fadin duniya.

Jaridar The Washington Post ta Amurka ta bayyana cewa, tun bayan barkewar annobar COVID-19 a kasar Sin, ba ma kawai gwamnatin kasar ta shawo kan cutar cikin sauri ba ne, har ma ta samar da tallafin kayayyakin kiwon lafiya ga sauran kasashe, duk wadannan sun kyautata kimar kasar Sin a idon al'ummun kasa da kasa, an lura cewa, kawo yanzu an kusan kammala aikin tantance wasu allurar rigakafin cutar a kasar Sin, a daidai wannan lokaci, kasar Sin ta shiga shirin, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da sauran kasashe domin ganin bayan annobar a fadin duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China