Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta hada kai da sauran kasashe don kara fadada muradu da makomar bai daya ta hanyar hadin gwiwa
2020-10-16 20:37:51        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana cewa, kasarsa za ta nace ga manufar bude kofa ta cin moriyar juna da yin aiki tare da sauran kasashe, don fafada muradu da cin gajiyar damammaki na bai daya ta hanyar yin hadin gwiwa.

Zhao Lijian, ya bayyana haka ne Jumma'ar nan yayin taron manema laraban da aka saba shiryawa, yana mai cewa, a ranar Alhamis din da ta gabata ce, aka bude bikin baje kolin Canton Fair na 128 a birnin Guangzhou ta kafar bidiyo, kwana guda bayan bikin cika shekaru 40 da kafuwar yankin tattalin arziki na musamman na Shenzhen, bikin baje kolin da ya samu halartar kamfanoni 26,000 daga sama da kasashe da yankuna 200, kuma yawan kayayyakin da aka baje ya zarce miliyan 2.4.

Ya ce, bikin baje kolin wani muhimmin dandali ne ga manufar kasar Sin ta bude kofa ga ketare da cinikayyar kasa da kasa. Shekaru 63 ke nan ana gudanar da baje kolin ba tare da katsewa ba, wanda ya taimaka wajen bunkasa musayar harkokin tattalin arziki da cinikayya da alaka tsakanin Sin da sauran kasashen ketare, da kara raya tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa.

Ya kuma nanata cewa, kasar Sin ba za ta daina aiwatar da manufarta ta yin gyare-gyare da bude kofa ba, haka kuma kasar Sin za ta kara bude kofarta ga kasashen waje.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China