Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An zabi kasar Sin mambar hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD
2020-10-14 20:30:03        cri

A jiya ne aka zabi kasar Sin a matsayin mambar hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD, na wa'adin shekarar 2021-2023, a zaben da aka gudanar a babban taron MDD karo na 75.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya shaidawa taron manema labarai Larabar nan cewa, zaben da aka yiwa kasar Sin, ya nuna yadda kasashen duniya suka yi na'am da manyan nasarorin da kasar ta Sin ta cimma a fannin kiyaye hakkin bil-Adam.

Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a hukumar kare hakkin bil-Adam ta MDD, da kara ba da gagarumar gudummawa a kokarin da ake na kare hakkin bil-Adama a duniya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China