Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bayyana goyon bayanta ga huldar kasa da kasa yayin taron MDD
2020-07-18 16:46:05        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya bayyana goyon bayan kasarsa ga tsarukan huldar kasa da kasa, ciki har da MDD, yayin da ake tunkarar kalubale da neman ci gaba na bai daya.

Wang Yi ya bayyana haka ne a jawabinsa mai taken "daukaka huldar kasa da kasa da gina al'umma mai makoma ta bai daya ga dan Adam", yayin wani taron manyan jami'ai na majalisar kula da tattalin arziki da zaman takewa ta MDD da aka yi wa taken "huldar kasa da kasa bayan annobar COVID-19: wane irin MDD ake bukata yayin cikar majalisar shekaru 75"

Wang Yi ya ce yayin da ake fuskantar sauye-sauyen da ba a taba gani ba cikin karni, kamata ya yi a karfafa rawar da MDD ke takawa maimakon raunanata, yana mai cewa, dole ne kuma a kare ikon majalisar.

Jami'in na kasar Sin, ya kuma gabatar da wasu shawarwari kamar haka:

Na farko, akwai bukatar kasashen duniya su daukaka tsarin huldar kasa da kasa da kin amincewa da daukar ra'ayi na kashin kai da kariyar cinikayya.

Na biyu, kasashen duniya na bukatar goyon bayan tsarin demokradiyya a batutuwan da suka shafi kasashen waje da kuma adawa da babbakere da neman iko.

Na uku, akwai bukatar kasashen duniya su kare zaman lafiyar kasa da kasa karkashin dokokin huldar kasashen waje da kuma adawa da haramtattun ayyuka da nuna fuska biyu.

Na hudu, ya kamata kasashen duniya su hada kai tare da goyon bayan juna da adawa da son kai da dabi'ar ci da gumin wasu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China