Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hutun mako guda na Sin ya nunawa duniya matsayin farfadowar attalin arzikin kasar
2020-10-12 16:45:20        cri
Tattalin arzikin kasar Sin ya kara samun farfadowa a yayin da aka samu bunkasuwar yawon shakatawa da karuwar hada hadar ciniki a lokacin da jama'ar kasar suka shafe tsawon mako guda don gudanar da hutun makon bikin ranar kafuwar kasar, kamar yadda tashar talabijin ta CNN ta bayyana cikin sharhinta na ranar Lahadi.

A lokacin hutun ranar kafuwar jamhuryar jama'ar kasar Sin, wanda ya fara daga ranar 1 ga watan Oktoba, kuma ya zo daidai da bikin tsakiyar kaka, lamarin da ya ba da damar gudanar da hutu har na tsawon kwanaki takwas.

Ya zuwa karshen wannann shekarar, ana hasashen gudunmawar da Sin zata bayar wajen bunkasar tattalin arzikin GDP na duniya zai iya karuwa da kashi 17.5 bisa 100, inda zai karu da maki 1.1, kamar yadda alkaluman shirin kasuwanci na CNN ya nuna, bisa amfani da alkaluman bankin duniya.

Kididdigar ta nuna cewa bankin duniya ya yi hasashen cewa GDPn kasar Sin zai iya karuwa da kashi 1.6 bisa 100 a wannan shekarar, yayin da tattalin arzikin duniya baki daya zai ragu da kashi 5.2 bisa 100.

Adadin kudaden shiga a fannin yawon shakawa a duk fadin kasar Sin zai kai yuan biliyan 466.56, kwatankwacin dala biliyan 69.7, kashi 69.9 bisa 100 na adadin makamancin lokacin shekarar 2019, kamar yadda ma'aikatar raya al'adu da yawon bude ido ta kasar ta sanar.

Oxford Economics, wata hukumar nazarin tattalin arziki ta kasar Birtaniya, ita ma ta nuna cewa, kasar Sin zata bunkasa tattalin arzikin GDP na duniya da kusan maki guda a wannan shekarar, kamar yadda ta wallafa a sharhinta, ta kara da cewa, tattalin arzikin Sin ya samu tagomashi ne sakamakon samun karuwar samar da kayayyaki ga kasuwannin duniya.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China