2020-10-14 10:21:08 cri |
Wata sanarwa da ofishin jakadancin Sin dake MDD ya fitar, ta ce Sin na godiya matuka ga kasashe mamabobin majalisar, saboda goyon bayan da suke bata, sannan ta taya sauran mambobin da aka zaba murna.
Hukumar wadda aka kafa a 2006, hukuma ce mai mambobi 47 dake karkashin MDD, wadda ke da nauyin kare hakkin dan adam. Babban zauren MDD ne ke zabar mambobin hukumar, sai dai ba za su iya yin tarce fiye da sau daya ba, sai dai bayan wani lokaci a sake zabensu.
An zabi kasar Sin a matsayin mambar hukumar har sau 5 wato a shekarar 2006 da 2009 da 2013 da 2016 da kuma 2020. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China