Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka da wasu kasashe sun yi rashin nasara a yunkurinsu na shafawa Sin bakin fenti
2020-10-07 16:55:55        cri
Amurka da wasu kasashe, sun kara rashin nasara a yunkurinsu na shafawa Sin bakin fenti dangane da batun hakkin bil adama, bayan a jiya Talata, kasashe da dama sun bayyana goyon bayansu ga Sin, yayin muhawarar kwamiti na 3 na babban zauren MDD.

Amurka da Jamus da Birtaniya da wasu kasashe sun zargi kasar Sin ba tare da wata hujja ba kan batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang da Hong Kong.

Zaunannen Wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya soki jawabai da kuma yunkurinsu na tsoma baki cikin harkokin gidan kasarsa, bisa fakewa da batun hakkin bil adama wanda ya haifar da fito na fito tsakanin kasashe mambobin majalisar.

Kusan kasashe 70 ne suka bayyana goyon bayansu ga matsayar kasar Sin, inda kasashen Pakistan da Cuba da Kuwait suka gabatar da jawabai kan batutuwan Xinjiang da Hong Kong da hakkin dan Adam, inda kowannensu ya wakilci wasu kasashe, don bayyan goyon bayansu ga kasar Sin. Haka zalika, wasu Kasashe da dama sun bayyana goyon bayansu ga kasar Sin a jawaban da suka gabatar.

Wadannan kasashe sun yabawa ci gaban da Sin ta samu a fannin kare hakkin dan Adam tare da goyon bayan kokarinta na kare cikakken 'yanci da tsaro da hadin kan kasar, da kuma adawa da siyasantar da batun hakkin dan Adam da fito na fito da kuma nuna fuska biyu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China