Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin watsa labarun ketare: Sinawa fiye da miliyan 500 ne suka yi tafiya yayin hutun bikin kasa, lamarin da ya nuna imanin kasar
2020-10-03 17:02:05        cri
Har zuwa yanzu, ana fuskantar yaduwar COVID-19 a duniya, amma Sinawa masu yawa sun yi tafiya a lokacin hutun bikin ranar kasa, wanda ya jawo hankulan wasu kafofin watsa labaru na kasashen ketare.

Kafafen yada labarai na CNN da AP da Bloomberg, da kuma sauran wasu takwarorinsu na kasashen ketare, sun ba da rahoto kan wannan lokacin hutun na bikin kasar Sin, inda suka amince cewa, kasar ta samu ci gaba sosai wajen yakar cutar COVID-19, sun kuma gano " karfin imanin" da kasar Sin ke nunawa.

 

Wani labarin da CNN ya bayar mai taken "Kasar Sin ta cimma nasarar kandagarkin cutar COVID-19, yanzu daruruwan miliyoyin mutane za su tafi hutu a lokaci guda", ya ruwaito adadin masu yawon bude ido na cikin gida a lokacin hutun ranar kasa da cibiyar kula da yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar: wato mutane miliyan 550, kuma ya bayyana bunkasar yawon bude ido a lokacin hutun a matsayin "imanin" da kasar Sin ta yi wajen dakile annobar.

 

 

Shi kuwa kamfanin dillacin labarai na AP ya ba da rahoton cewa, baiwa mutane masu dimbin yawa damar tafiye-tafiye cikin 'yanci a cikin kasar, abu ne da ba za a iya samu ba a sauran sassan duniya. A cewar rahoton, saboda yadda ake shawo kan cutar, yawan masu yawon bude ido zuwa manyan wuraren shakatawa a kasar Sin a rubu'i na biyu na bana, ya haura da kusan kashi 159% bisa na rubu'i na farko.

 

 

Kamfanin dillancin labarai na Bloomberg ya ruwaito cewa, a wannan makon, shugabannin kamfanonin jiragen sama dake wurare daban daban a duniya da suka fuskanci kalubale, za su sanya "idanun kishi" kan kasar Sin, saboda miliyoyin mutane za su yi tafiya ta jirgin sama a lokacin hutun bikin kasa, hakan zai sa kamfanonin jiragen sama na kasar su yi gaba sosai wajen kawar da tasirin da annobar ke kawowa, da maido da ayyukansu na yau da kullum. A cewar rahoton, wannan makon zai samar da karin kwarin gwiwa ga farfadowar tattalin arzikin kasar. (Mai fassara: Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China