Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AfDB: Yankin kudu da saharar Afirka na da kasuwar lantarki da ta kai dalar Amurka biliyan 3.6
2020-10-08 16:51:46        cri
Bankin raya Afirka na AfDB, ya ce yankin kudu da saharar Afirka, na da kasuwar lantarki da ake samarwa daga kananan cibiyoyi, da ta kai ta dalar Amurka biliyan 3.6. Bankin ya ce hakan ya samu ne sakamakon kyautatuwar tsare tsare, da manufofi, tare da kirkire kirkiren fasaha da yankin ke samu.

Da yake tsokaci ta kafar bidiyo game da wannan batu, darakta a fannin cinikayyar makamashi na bankin Wale Shonibare, ya ce hanya mafi arha da kasashen shiyyar za su bi domin samun isasshiyar wutar lantarki, da biyan bukatun sabbin masu bukatar lantarkin nan da shekara ta 2030, ita ce gaggauta gina kananan cibiyoyin samar da lantarki, da hanyoyin rarraba shi.

Mr. Shonibare wanda ke jawabi yayin taron masu ruwa da tsaki game da samar da kudaden cikayya, da nazarin yadda tsare tsaren fannin na lantarki ke gudana a Afirka, ya ce bisa kiyasi, akwai al'ummun Afirka miliyan 600 da ba sa samun lantarki, don haka ake da bukatar gaggauta hade nahiyar da ababen more rayuwa da suka shafi fannin musamman a mataki na shiyya-shiyya, ta yadda za a iya rika sayar da ragowar lantarkin da ake samarwa ga yankuna masu bukata.

A shekarun 1890 ne aka fara kafa irin wadannan cibiyoyi, inda kasar dimokaradiyyar Congo ta zamo ta farko da ta ci gajiyar hakan, yayin da kuma kasashen Habasha da Najeriya ke kan gaba wajen cin gajiya daga kasuwannin lantarkin da irin wadannan cibiyoyi ke samar wa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China