Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci a gaggauta karbe haramtattun makamai a Afrika
2020-09-06 16:01:14        cri
Kungiyar tarayyar Afrika AU, tace akwai bukatar a gaggauta karbe dukkan makamai daga hannun fararen hulda da aka mallake su ba bisa ka'ida ba a Afrika. A bisa kiyasi, akwai makamai kusan miliyan 40 dake hannun fararen hula a nahiyar ta Afrika.

Kwamishinan kula da zaman lafiya da tsaro na kungiyar AU, Smail Chergui, ya bayyana hakan ne a sanarwar da aka bayar dangane da watan da aka kebe game da shirin ajiye makamai na Afrika, wanda taken shirin na AU na shekarar 2020 shine "Kawar da karar bindiga: Domin samar da ingantaccen cigaban Afrika".

Kebe watan raba Afrika da makamai, ya kasance wani muhimmin jigo na manufofin kungiyar tarayyar Afrika dangane da daukar matakai na zahiri don kawar da harbe harben bindga a Afrika, an ayyana shirin ne a lokacin taron kolin AU karo na 29 wanda aka gudanar a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha a watan Yulin shekarar 2017, inda aka ware watan Satumbar kowace shekara a matsayin watan shirin mika haramtattun makamai.

A cewar kungiyar AU, an kiyasta makamai miliyan 40 wadanda fararen hula suka mallaka a nahiyar Afrika, kuma shine kashi 80% na dukkan makaman dake nahiyar.

Daga cikin makaman miliyan 40 dake hannun fararen hula, miliyan 5.8 ne kadai aka yi musu rejista a hukumance, yayin da kusan miliyan 16 ba a yi musu rejista ba. A cewar AU, ragowar makaman sama da miliyan 18 ba a tantance hakikanin yadda suke ba.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China