Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane kimanin miliyan 13.4 dake tsakiyar yankin Sahel na bukatar agajin jin kai in ji MDD
2020-09-16 11:01:30        cri
Ofishin MDD mai lura da ayyukan jin kai ko OCHA a takaice, ya ce mutane miliyan 13.4 dake zaune a yankunan tsakiyar Sahel, na bukatar agajin jin kai da kariya, sakamakon tashe tashen hankula daban daban da suke fuskanta.

Ofishin na OCHA ya ce ga misali, alkaluman kamfar abinci sun ninka har rubi hudu a kasar Burkina Faso, sun kuma ninka kusan sau biyu a Mali, yayin da suka daga da kaso 77 bisa dari a janhuriyar Nijar, idan an kwatanta da shekarar da ta gabaci haka. Dukkanin wadannan sun kara fadada yanayin matsi da al'ummun kasashen ke fuskanta.

Kaza lika ofishin ya ce a yanzu haka, akwai mutane miliyan 6.6, dake fuskantar matukar kamfar abinci a wannan yanki, da kuma masu gujewa muhallansu a kasashen Burkina Faso, da Mali da yammacin Nijar, wadanda yawan su ya kai miliyan 1.4, adadin da ya kasance kari kan mutane 70,000 da ake da su a shekaru biyu da suka gabata.

A hannu guda kuma, OCHA ya ce ana fuskantar wahalhalu wajen isa ga wadanda ke cikin matukar bukata, sakamakon kalubalen tsaro, ciki hadda hari kan fararen hula, da jami'an ba da agaji da ake fuskanta.

Bugu da kari, matsalar sauyin yanayi, ta dada dagula al'amura, inda sama da mutane 500,000 ke fuskantar ambaliyar ruwa a Burkina Faso, da Mali da kuma Nijar. Ana kuma bukatar kudi har dalar Amurka biliyan 1.4, don tallafawa wadannan kasashe uku, a gabar da ofishin ke fuskantar karancin kudade.

An dai shirya kaddamar da gidauniyar neman taimako, yayin taron ministoci da za a gudanar a kasar Denmark, a ranar 20 ga watan Oktoban wannan shekara. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China