Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin da wasu kasashe 26 sun soki Amurka da wasu kasashen yamma kan laifin take hakkin bil-Adama
2020-10-06 16:13:51        cri
A jiya ne, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya gababar da wata sanarwar hadin gwiwa, yayin babban taron muhawarar MDD a madadin kasashe 26, inda a cikinta suka soki kasar Amurka da wasu kasashen yamma, kan yadda suke take hakkin bil-Adama.

Sanarwar ta kuma yi kira da a gaggauta dage takunkuman da aka kakabawa wasu kasashe bisa radin kai, tare da bayyana damuwa kan yadda wadannan kasashe ke nunawa wasu rukunonin jama'a wariyar launin fata.

Zhang ya ce, annobar COVID-19 na ci gaba da yiwa kasashen duniya illa, musamman kasashe masu tasowa. Matakan yaki da annobar da farfadowa bayanta, na bukatar sadaukar da kai da hadin gwiwar kasa da kasa. Sai dai kuma kasashen duniya na ci gaba da ganin yadda ake aiwatar da ra'ayi na kashin kai, wadanda suka saba dalilin kafa MDD da ka'idojinta, da dokoki na kasa da kasa, da cudanyar bangarori daban-daban, da muhimman ka'idojin alakar kasa da kasa.

Ya ce, kusan shekaru 20 ke nan bayan fara amfani da yarjejeniya da shirye-shiryen Durban, abubuwa marasa kyau kamar kisan George Floyd da harbin Jacob Blake na ci gaba da faruwa, a hannu guda kuma, rukunin mutane masu rauni na ci gaba da dandana kudarsu ko rasa rayukansu baya ga cin zarafi a hannun 'yan sanda.

A don haka, jami'in na kasar Sin, ya ce, "suna maraba da ganin an fara amfani da kudurin da hukumar kare hakkin bil-Adama ta zartas wato ' Yayata da kare hakkin bil-Adama da muhimman 'yancin 'yan Afirka da masu tsatson Afirka daga amfani da karfin tuwo da sauran nau'o'in take hakkin bil-Adama da jami'an tsaro ke aikatawa', tare da kira na ganin an aiwatar da kudirin baki dayansa."(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China