2020-10-01 16:41:51 cri |
Guterres, ya bayyana a taron kolin MDD kan halittu cewa, kiyaye halittu da kiyaye muhallin halittu suna da matukar alfanu ga cigaban rayuwar dan adam da makomarsa. Wasu muhimman ginshikai ne wajen cimma nasarar samun dawwamamman cigaba da kuma aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris.
Har yanzu, duk da irin jaddada kudiri da ake yi kan batu, amma babu wani cikakken kokari da aka aiwatar domin cimma muradin shirin kare halittu na kasa da kasa da ake burin cimmawa zuwa shekarar 2020. Ya kamata a kara himma, ba wai daga bangaren gwamnatoci kadai ba, har ma da bangarorin masu ruwa da tsaki a cikin al'umma.
Jami'in MDDr yayi gargadin cewa, gurbata tsarin yanayi muhallin halittu ba yana shafar batun muhalli kadai ba ne, har ma yana shafar batutuwan tattalin arziki, kiwon lafiya, hakkokin 'yan adam, da kuma 'yancinsu.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China