2020-09-23 11:14:32 cri |
Chen Xu ya bayyana cewa, kimanin mutane miliyan 800 ne suke fama da talauci a duniya, musamman bayan barkewar cutar COVID-19, kuma akwai yiwuwar mutane miliyan 71 za su sake fadawa kangin talauci. Hakan zai tsananta matsalar rashin daidaito a cikin al'umma, da kawo illa kan yadda ake kiyaye hakkin dan Adam a duniya baki daya.
A don haka, Chen Xu ya yi kira ga kasashen duniya, da su ba da muhimmanci ga aikin yaki da talauci don bunkasa tattalin arziki, da taimakawa yaki da talauci ta sabbin hanyoyi a lokacin da bukatar hakan ta taso, da sa kaimi ga yaki da talauci, da bunkasa tattalin ariki da zamantakewar al'umma da al'adu, da kiyaye muhalli, da kuma kiyaye hakkin dan Adam baki daya. Kana ya yi kira ga kasashen duniya, da su maida hankali kan bukatun jama'a, ta hanyar inganta rayuwarsu, da bullo da tsarin bada inshora ga zamantakewar al'umma, da rage tasirin da masu fama da talauci suka fuskanta a sakamakon cutar COVID-19, da kara gina ayyukan more rayuwa a yankuna masu fama da talauci, da samar da hidimar kiwon lafiya, da bada ilmi, da al'adu, da likitanci ga masu fama da talauci, da kuma kara samar musu da ayyukan yi, don kara karfinsu na dogaro da kai. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China