Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe da dama sun soki lamarin ra'ayin kashin kai a taron hukumar kare hakkin dan Adam
2020-09-24 16:11:31        cri

A ranar 22 ga watan Satumba, yayin taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 45, an yi muhawara inda wakilan kasashe mahalarta taron suka tabo batu game da mummunar illar da ra'ayin amfani da karfin tuwo na bangare guda yake haifarwa ga hakkin dan Adam. Wakilan sun hada da na kasashen Syria, Iraqi, Botswana, Zimbabwe, Sudan da Masar, sun bayyana cewa, ra'ayin bangare daya na nuna karfin tuwo mataki ne dake haifar da mummunar illa ga hakkokin dan Adam na 'yancin rayuwa, da na lafiya da kuma samun kyakkyawar rayuwa ga mutanen dake kasashen da aka kakabawa takunkumi, lamarin da ke haifar da damuwa ga kasashen da lamarin ya shafa wajen rashin samun muhimman kayayyakin kula da lafiyar jama'a akan lokaci, ta yadda rukunin mutane marasa galihu kamar mata, da kananan yara, da masu bukata ta musamman, suna dandana kudarsu matuka.

Wakilin kasar Sin ya bayyana cewa, wasu kasashen suna daukar matakan gallazawa na kashin kansu kamar kakaba takunkumin tattalin arziki da na kudade ga sauran kasashe, wanda hakan yake da babbar illa game da tsarin siyasa da na tattalin arzikin kasa da kasa da kuma tsarin tafiyar da harkokin duniya. Hukumar kare hakkin dan Adam da wakilai na musamman masu shiga tsakani ya dace su bukaci kasashen duniya da lamarin ya shafa da su yi watsi da aniyar daukar matakan gallazawa na nuna ra'ayin kashin kai, kuma bai kamata a dauki duk wasu matakai dake keta hakkin dan Adam ko kuma hakkin alumma ba.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China