Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kowa Ya kashe Wutar Gabansa
2020-09-30 18:50:01        cri

Mai daki aka ce, shi ya san inda yake masa Yoyo, kuma ba dole ba ne sai wata kasa ta bi umarnin wata kasa game da wasu fannonin tafiyar da harkokin kasarta, ko manufofi ko tsare-tsare da sauransu ba.

Kalaman da mahukuntan kasar Sin suka gabatar a kwanakin baya cewa, ba za ta karbi wani umarni daga wadanda suka nada kansu a matsayin malamai a fannin kare hakkin bil Adama ba, jirwaye ne mai kamar wanka.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya zargi kasashen Sin, da Iran, da Venezuela da wasu karin kasashen, da laifin keta hakkokin bil Adama. Wai kura ce za ta cewa Kare Maye.

Amurka dai ta sha nada kanta malamar kare hakkin bil Adama, tare da zargin sauran kasashe da keta hakkin bil Adama. Duk da cewa Amurkan na cikin mummunan yanayi na kare hakkin bil Adama, ta kan kuma yada jita-jita da neman bata sunan kasashe kan abin da bai shafe ta ba.

A baya-bayan nan ma kasashe masu tasowa, sun fito karara inda suka soki kasar Amurka da kungiyar tarayyar Turai da kasashen Jamus, da Finland, da Sweden da Norway, kan yadda suke tafiyar da batutuwan da suka shafi kare hakkin bil-Adama.

 

 

Shi dai Pompeo, ya bukaci Amurka da jami'an ta, wai su yi taka tsantsan da jami'an diflomasiyyar kasar Sin, don kaucewa amfani da su wajen yada farfagandar Sin da ma leken asiri. Abin da Amurkar take yi, shi take tunanin haka sauran kasashe ma suke yi, Gwano dama aka ce ba ya jin Warin jikinsa.

Sai dai, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya ce 'yan siyasar Amurka na fama ne da dimuwa sakamakon kin jinin Sin, kuma kasar Sin ba ta taba damuwa da harkokin cikin gidan Amurka ba.

Sanin kowa ne cewa, kasar Sin ba ta tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe ko gindayawa wata kasa tsari ko ka'idar tafiyar da harkokin kasarta ba. Don haka, duk wata kasa mai cikakken 'yanci, kamar kasar Sin, ba za ta lamunci yadda kasashen yamma musamman Amurke za ta rika yi mata shisshigi kan yadda take tafiyar da al'amuranta ba. Iya Ruwa aka ce fidda kai.

Kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana ne, kasashen duniya, manya ko kanana, masu karfi ko masu rauni, matsayin su guda ne a dandali na kasa da kasa. Kuma wadanda ke ganin suna da karfin da zai ba su ikon karya ka'idojin kasa da kasa, za su rasa abokan tafiya a nan gaba. Yanzu fa kan Mage ya waye. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China