Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa CDC ta bukaci a guji yin sakaci da matakan kandagarki yayin da ake sassauta dokar kulle
2020-08-23 15:42:47        cri

Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Africa CDC, ta bukaci kasashen nahiyar Afrika su guji yin sakaci kan matakan kandagarkin hana yaduwar annobar COVID-19.

Kiran na gaggauwa ya zo ne daga daraktan Afrika CDC, John Nkengasong, wanda ya bayyana cewa, ana samun raguwar yaduwar annobar COVID-19 a nahiyar, lamarin da ya bayar da gwarin gwiwa wajen raguwar bazuwar cutar.

Sai dai daraktan na Africa CDC, ya gargadi nahiyar cewa, ya kamata a yi hattara wajen tabbatar da ana yin amfani da takunkumin rufe fuska, da bayar da tazara, kuma a kara yawan gwaje gwajen da ake yi, duk da cewa wasu kasashen sun fara sassauta matakan kulle.

Nkengasong ya ce, "Ba mu son mutane su yi sakaci game da matakan kandagarki," ya kara da cewa, ana fama da wata irin shu'umar kwayar cuta wacce za ta iya sake bazuwa cikin sauri, kamar yadda ake gani a wasu sassan duniya.

Alkaluman da Afrika CDC ta fitar ya nuna cewa, a 'yan makonnin da suka wuce, an samu raguwar yawan masu kamuwa da cutar a Afrika inda aka samu sabbin masu kamuwa da cutar 10,344 a rana guda, idan an kwatanta da 11,494 da aka samu a makon jiya da kuma 14,447 da ake samu a wasu makonnin baya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China