Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta bukaci a samar da daidaito game da tsarin samar da rigakafin COVID-19 a Afrika
2020-09-04 10:21:02        cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bukaci masu bayar da gudunmawa da kamfanoni su samar da isassun kudade domin baiwa kasashen Afrika damar samun ingantattun rigakafin annobar COVID-19.

Richard Mihigo, manajan shirin samar da alluran rigakafi na hukumar WHO, ya ce kamata ya yi bukatu da kuma burin da kasashen Afrika ke da shi ya samu karbuwa matuka kan kokarin hadin gwiwa da kasa da kasa ke yi na samar da alluran rigakafin annobar.

Mihigo, ya fadawa taron manema labarai ta kafar bidiyo a Nairobi cewa, a mafi yawan lokuta, Afrika tana sahun baya game da shirin samar da alluran rigakafi, amma a wannan karo bai kamata hakan ta faru ba, yayin da aka shiga wani muhimmin matakin yaki da annobar COVID-19.

Ya kara da cewa, dole ne a samar da isassun alluran rigakafin kuma a ba da fifiko ga jami'an lafiya dake bakin aiki, da tsoffi, da sauran mutane dake fama da wasu matsalolin lafiya a nahiya.

Jami'in na WHO ya ce, dukkan kasashen Afrika 54 sun sanya hannu kan yarjejeniyar COVAX, wani shiri ne wanda hukumar WHO ta bullo da shi tare da hadin gwiwar gamayyar bangarorin dake yunkurin samar da rigakafin wato GAVI, da gamayyar shirin yaki da annobar wato CEPI, wadanda suka lashi takobin samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 miliyan 220 ga nahiyar Afrika.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China