Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Zimbabwe ta zargi kasashen yamma da amfani da 'yan adawa a yunkurin tada zaune tsaye
2020-09-29 10:03:44        cri

Gwamnatin Zimbabwe, ta zargi wasu kasashen yammacin duniya da amfani da magoya bayan jam'iyyun adawar kasar, da kungiyoyin gama kai, a wani yunkuri na tada zaune tsaye.

Da yake tabbatar da wannan zargi jiya Litinin, karamin ministan tsaron kasar Owen Ncube, ya shaidawa 'yan jarida cewa, wasu daga gwamnatocin kasashen yamma, na aiki da bata-garin 'yan kasar, don kafa wata kungiya ta masu dauke da makamai, tare da fasa kwaurin bindigogi zuwa cikin kasar. To sai dai kuma ministan ya ki amsa tambayoyin da 'yan jaridar suka yi masa, bayan furta wannan zangi.

Kaza lika Mr. Owen ya ce suna lura da kokarin da wasu suke yi, na jefa Zimbabwe cikin yamutsi. Amma a cewar sa, sashen tsaron kasar zai dauki managartan matakai, na dakile wannan barazana. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China