Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin Sin sun ba da gudunmuwar kayayyakin lafiya ga Zimbabwe domin yaki da COVID-19
2020-06-27 16:11:30        cri

Kamfanonin gwamnatin kasar Sin dake aiki a Zimbabwe, sun ba da gudunmuwar kayayyakin lafiya da darajarsu ta kai dala dubu 55, domin taimakawa kasar a yakin da take da annobar COVID-19.

Kamfanonin masu aiki karkashin inuwar kungiyar kamfanonin kasar Sin a Zimbabwe, sun ba da magunguna ga rukunin asibitocin Parirenyatwa da makarin baki da hanci ga larduna daban-daban da hukumomin kula da shige da fice da na tattara kudin shiga na kasar.

Babban asibitin kasar Parirenyatwa, ya karbi magungunan da darajarsu ta kai dala 5,000, hukumar shige da fice ta karbi makarin baki da hanci 40,000, hukumar tattara kudin shiga kuma ta karbi makarin 20,000, yayin da lardin Matabeleland na kudu da lardunan tsakiyar kasar, suka karbi makarin baki da hanci 20,000 kowannensu.

Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa ne ya karbi kayayyakin a fadarsa. Ya kuma godewa kamfanonin bisa gudunmuwar, yana mai cewa, za su taimakawa kasar a yakin da take da annobar.

Ya ce gudunmuwar daga kasar Sin, da sauran masu ba da gudunmuwa, ta taimaka wajen bunkasa karfin kasar na tunkarar annobar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China