Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zimbabwe ta dakatar da harkokin majalisar dokokin kasar bayan 'yan majalisar 2 sun kamu da COVID-19
2020-07-28 09:43:15        cri

Akawun majalisar dokokin Zimbabwe, Kennedy Chokuda, ya sanar da dakatar da galibin harkokin majalisar bayan mambobinta 2 sun kamu da cutar COVID-19.

Kennedy Chokuda ya sanar a jiya cewa, direban bus dake jigilar mambobin kwamitin majalisar kan ma'aikatu a fadin kasar da wani dan jarida dake tafiya tare da su, su ma sun kamu da cutar.

A cewarsa, mambobin na daga cikin ayarin dake rangadi a fadin kasar. Kuma yanzu haka, duk wanda ke cikin ayarin ya killace kansa, kamar yadda ka'idojin ma'aikatar lafiya ta kasar suka tanada.

Kennedy Chokuda ya kara da cewa, zaman majalisar na yau Talata, zai gudana ne da kayaddadun mambobi, wanda zai mayar da hankali kan dage zaman zuwa wani lokaci.

Ya bayyana cewa, wannan zai ba da damar tsaftacewa da feshin kafatanin ginin majalisar, da kuma bibiya da gwada wadanda suka yi mu'amala da mambobin majalisar da suka kamu da cutar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China