Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An rufe baje kolin masana'antun kasa da kasa na kasar Sin na 2020 a Shanghai
2020-09-20 16:21:24        cri
A ranar Asabar aka kammala bikin baje kolin masana'antun kasa da kasa na kasar Sin karo na 22 wato CIIF, a birnin Shanghai, inda aka samu sabbin kayayyakin fasahohi kusan 500 da suka baje hajojinsu a tsawon kwanaki biyar.

Taken bikin ba bana shi ne "Kirkire-kirkire da kulla alakoki don samar da sabon cigaban masana'antu," a bikin baje kolin na CIIF na wannan shekarar, an samu karin kwararru da suka mahalarta da kashi 4.3 bisa 100, sannan bikin ya ja hankalin 'yan kasuwa da suka baje hajojinsu kimanin 2,238 daga kasashe da shiyyoyin duniya 22, kusan kashi 20 bisa 100 na mahalartan sun fito ne daga kasashen ketare ko kuma kamfanonin baki 'yan kasashen waje dake kasar Sin.

Pang Xingjian, mataimakin shugaban kamfanin Schneider Electric, ya ce tattalin arzikin duniya yana cike da manyan kalubaloli sakamakon annobar COVID-19, kuma a lokacin da ake fuskantar halin rashin tabbas, kamfanin yana fatan kaddamar da sabbin manhajojinsa a karon farko a kasar Sin.

A shekarar 1999 aka kaddamar da bikin bajekolin CIIF karo na farko, bikin ya kasance daya daga cikin muhimman dandalolin dake janyo hankulan 'yan kasuwar kasa da kasa, da kulla alakar cinikayya, gami da kulla hadin gwiwa a fannin masana'antu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China