Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An nada tsohon ministan wajen Mali firaministan rikon kwarya
2020-09-28 09:48:54        cri

Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Mali Mr. Bah N'Daw, ya nada tsohon ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar Moctar Ouane, a matsayin firaministan rikon kwarya karkashin dokar shugaban kasa.

An haifi Mr. Ouane ne a shekarar 1955, ya kuma kasance jakadan Mali a MDD tsakanin shekarar 1995 zuwa 2002. Kaza lika ya rike mukamin ministan harkokin wajen kasar karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasar Amadou Toumani Toure.

Kafin nadin sa firaministan rikon kwaryar, Ouane babban jami'i ne a tawaga mai rajin wanzar da zaman lafiya da tsaro, karkashin hukumar bunkasa tattalin arziki da hada hadar kudade ta yammacin Afirka ko UEMOA a takaice.

Bisa kudurin kafa gwamnatin rikon kwarya da wakilai 500 masu wakiltar sassan jami'iyyun siyasa daban daban na kasar suka cimma, wajibi ne Ouane ya kafa gwamnatin rikon kwaryar da mambobin ta ba za su zarta 25 ba.

Bayan rantsar da shugaba Bah N'Daw, kungiyar raya yammacin Afirka ta ECOWAS, ta sanar da dage takunkumin da ta kakabawa Mali, bisa alkawarin mika mulkin kasar da sojoji suka yi, hannun gwamnatin rikon kwarya da firaministan ta zai kasance farar hula. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China