Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kiwon kaji ya baiwa mutanen Ningdu damar samun walwala
2020-09-27 15:15:48        cri

Gundumar Ningdu dake lardin Jiangxi na kasar Sin ta shahara sosai, bisa wani nau'in kaji na musamman da ake samarwa a can, da ake kira kajin "San Huang".

A wannan gunduma akwai dazuka masu yawa, inda muhallin ya dace da rayuwar kaji. Chen Xiaobao, wani dan gundumar ne, wanda ya riga ya kwashe shekaru 27 yana kiwon kaji. A cewarsa, za a iya kiwon wannan nau'in kajin, na tsawon kwanaki 270, kafin a yankasu a kuma sayar da namansa. Abincin kajin, shi ne masara, da ciyayi, gami da tsutsa da kwari dake cikin filin ciyayi. Wadannan abinci sun sa naman kajin samun inganci sosai.

A lokacin da ya fara kiwon kajin, ya kan samar da kaza kimanin 600 a kowace shekara. Zuwa yanzu yana samar da kaza fiye da dubu 350 a duk shekara, tare da samun kudin da ya wuce Yuan miliyan 10. Sauran masu kiwon kaza su ma sun samu wadata sosai.

Yanzu a gundumar Ningdu da yawan al'ummarta ya kai dubu 800, yawan mutane masu sana'ar kiwon kaji ya kai fiye da dubu 20, wadanda suke samar da kaji miliyan 90 a kowace shekara. Darajar kajin ta kai Yuan biliyan 2.7. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China