Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi: A kara kokarin raya yankunan dake kudancin jihar Xinjiang
2020-09-26 21:43:35        cri
A wajen taron karawa juna sani dangane da batun jihar Xinjiang da ya gudana tsakanin ranekun 25 zuwa 26 a birnin Beijing, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ce, raya tattalin arzikin jihar Xinjiang shi ne tushen tsaron yankin. Saboda haka, a cewarsa, za a yi amfani da manufar kasar ta raya cibiyoyin tattalin arziki dake kan hanyar siliki, da ta bunkasa yankunan yammacin kasar ta hanyar bude kofa, wajen taimakawa raya jihar Xinjiang. Amma dole ne a tabbatar da cewa ba za a gurbata muhallin jihar ba.

Haka zalika, shugaban ya jaddada muhimmancin kawar da talauci, da samar da karin guraben aikin yi a jihar. Da kuma kyautata tattalin arziki da zaman rayuwar jama'a a kudancin jihar ta Xinjiang. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China