Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi gargadin cewa makarkashiyar Amurka ta hadin gwiwa da Taiwan ba za ta yi nasara ba
2020-09-21 19:56:46        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce duk wata makarkashiya da Amurka ke kullawa, ta fuskar yin hadin gwiwa, da tallafawa yankin Taiwan na kasar Sin ba za ta yi nasara ba.

Wang ya yi wannan gargadi ne, a yayin taron manema labarai na yau Litinin, yana mai cewa ziyarar da wasu jami'an Amurka suka kai yankin Taiwan, wani mataki ne na tsokanar siyasa, dake da nufin ingiza masu rajin neman 'yancin Taiwan, ta yadda 'yan awaren za su samu karin karfin gwiwar ta da zaune tsaye, kuma hakan zai gurgunta alakar Sin da Amurka, da ma zaman lafiya da daidaito a zirin Taiwan.

Jami'in ya kara da cewa, Sin na matukar adawa da wannan mataki. Kaza lika bangaren Sin na jan kunnen Amurka, cewar manufar samun 'yancin Taiwan ba za ta taba yin nasara ba.

A hannu guda kuma, Sin za ta ci gaba da nacewa manufar kare ikon mulkin kai, da yankunanta, za ta ci gaba da adawa da tsoma bakin kasashen waje cikin harkokin gidanta, kana za ta hade kan dukkanin yankunan dake zirinta.

Bugu da kari, Sin za ta himmatu wajen yakar duk wani mataki na yunkurin gurgunta moriya, da harkokin cikin gidan ta. Kuma ba wani karfi da zai iya dakile ikon Sin na sake dinkewa waje guda. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China