Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ba ta bukatar "malaman kare hakkin dan Adam"
2020-09-24 20:51:10        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce Sin ba za ta karbi wani umarni daga wadanda suka nada kansu malamai a fannin kare hakkin bil Adama ba, kuma kamata ya yi Amurka ta dukufa wajen warware matsalolin dake gabanta. Wang ya yi wannan tsokaci ne a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai na rana-rana da ake gudanarwa.

Wasu rahotannin baya bayan nan sun hakaito sakataren wajen Amurka Pompeo, yana zargin kasashen Sin, da Iran, da Venezuela da wasu karin kasashen, da laifin keta hakkokin bil Adama. Game da hakan ne kuma Mr. Wang Wenbin ya amsa tambayar da aka yi masa, inda ya ce Amurka ta sha nada kanta malamar kare hakkin bil Adama, tare da zargin sauran kasashe da keta hakkin bil Adama. Duk kuwa da cewa Amurkan na cikin mummunan yanayi na kare hakkin bil Adama.

Bugu da kari, a cewar rahoton, Mr. Pompeo ya bukaci Amurka da jami'an ta, da su yi taka tsantsan da jami'an diflomasiyyar kasar Sin, don kaucewa amfani da su wajen yada farfagandar Sin da ma leken asiri. Da yake maida martani game da hakan, Wang Wenbin ya ce 'yan siyasar Amurka na fama ne da dimuwa sakamakon kin jinin Sin, kuma kasar Sin ba ta taba damuwa da harkokin cikin gidan Amurka ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China