Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD da AU za su karfafa alaka a tsakaninsu
2019-05-07 10:54:54        cri

MDD da kungiyar tarayyar Afirka (AU) za su karfafa alaka a tsakaninsu wajen ganin sun aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwar sassan biyu a fannin zaman lafiya da tsaro da ajadar samun ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030, da ajadar AU game da raya nahiyar Afirka nan da shekarar 2063.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres da shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka (AU) Moussa Faki Mahamat sun yi maraba da wannan mataki, kamar yadda yake kunshe cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka bayar, bayan taron MDD da AU na shekara-shekara karo na uku da ya gudana a hedkwatar MDD dake birnin New York na kasar Amurka.

Jami'an sun kuma bayyana kudurinsu, na ci gaba da zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu, wajen magance batutuwan da suka shafi zaman lafiya da tsaro da cimma nasarar manufofin ci gaba mai dorewa a Afirka ta hanyar daukar karin matakan da suka dace.

Sanarwar ta kara da cewa, ci gaba da yin hadin gwiwa wajen ganin an aiwatar da yankin cinikyayya cikin 'yanci na Afirka da sauran batutuwa masu nasaba da hakan, ciki har da yarjejeniyar zirga-zirgar cikin 'yanci da kasuwar sufurin sama ta bai daya ta Afirka na daga cikin batutuan da aka tattauna, saboda rawar da za su taka wajen bunkasa hadewar yankin, da karfafa ci gaban tattalin arziki, da samar da guraben ayyukan yi ga matasan Afirka, da kawar da talauci, matakan da ake fatan za su kai ga samar da zaman lafiya a cikin al'umma.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China