Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MOC: Daidaita wasu sassan zuba jari da kasar Sin ta yi ba ya nufin wata kasa ko kamfani
2020-09-25 10:08:14        cri
Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin (MOC) ta bayyana cewa, matakan da kasar ta dauka na takaita zuba jari a wasu sassa, ba ta yi haka ne don wata kasa ko kamfani ba.

Mai magana da yawun ma'aikatar Gao Feng wanda ya sanar da haka yayin wani taron manema labarai da ma'aikatar ta shirya, ya ce, sana'o'i da suka fada cikin jerin sunayen, ya dogara ne kan irin ayyukan da suke gudanarwa, ba wai an zabe su ne don kawai a sanya su cikin jerin sunayen ba

Gao ya kara da cewa, za a ci gaba da daukar matakai bisa doka, kan jerin sunayen sana'o'in da suka fada cikin wannan shiri yadda ya kamata. Ya kuma sake nanata kudurin gwamnatin kasar Sin, na ci gaba da zurfafa gyare-gyare da bude kofarta ga kasashen ketare, haka kuma manufarta na kare hakki da muradun 'yancin kasuwanni, ba zai canja ba. A don haka, ya ce, bai kamata kamfanonin waje masu gaskiya da martaba doka, su nuna wata damuwa ba.

A ranar 19 ga watan Satumba ne, ma'aikatar cinikayyar kasar Sin, ta fitar da ka'idoji game da wasu sassa na sana'o'i da aka takaita zuba jari a cikinsu, matakin da ya fara aiki nan take.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China