![]() |
|
2020-09-21 19:43:49 cri |
Majalissar gudanarwa ta kasar Sin ta sanar da fitar da wani babban shirin kafa sabbin yankunan cinikayya maras shinge na gwaji guda uku, a birnin Beijing, da lardunan Hunan da Anhui, a gabar da ake kara daga manufar kasar ta bude kofa ga kasashen waje zuwa mataki na gaba.
Tsarin ya fayyace fifikon kowane yanki, zai kuma samar musu da babbar damar aiwatar da sauye-sauye, ta yadda yankunan za su iya zurfafa bincike da fadada bude kofa. (Saminu Alhassan)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China