Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala bikin baje kolin hada-hadar ba da hidima na kasa da kasa na kasar Sin cikin nasara
2020-09-09 20:58:30        cri

A yau Laraba ne aka kammala bikin kasa da kasa na baje kolin hada-hadar ba da hidima na kasar Sin na shekarar 2020 a nan birnin Beijing.

Mashirya bikin sun ce an cimma manyan nasarori yayin baje kolin na bana, ciki hadda sanya hannu kan yarjejeniyoyi 240, an kuma cimma wasu sakamako 97 a hukumance, tare da gabatar da wasu sabbin kirkire kirkire 99 da aka cimma nasarar su.

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, kamfanoni 5372 na gida da na kasashen waje sun kafa runfunansu a shafin intanet, an kuma gudanar da taruka 32 ta yanar gizo, tare da taruka 173 kai tsaye ta bidiyo. Kaza lika an gabatar da shirye-shirye har 1870 ta yanar gizo, baya ga tattaunawar cimma matsaya har sau 550,000 wadanda aka gudanar ta yanar gizo, ciki hadda wasu 145, 000 daga kasashen ketare, wadanda suka kai kaso 26.4% na jimillar tattaunawar cimma matsayar da aka gudanar yayin baje kolin. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China