Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta amince da sabon aikin gina layin dogo
2020-09-25 09:56:08        cri

Gwamnatin Najeriya ta amince da kashe dala biliyan 1.96 domin gudanar da aikin gina sabon layin dogo wanda zai hade Najeriyar da jamhuriyar Nijer.

An bayyana daukar wannan mataki ne a ranar Laraba, bayan kammala taron majalisar zartarwar kasar dake gudana a kowane mako wato FEC, wanda shugaban kasar Muhammadu Buhari ya jagoranta, inda ya samu halartar ministoci a Abuja, babban birnin kasar.

Ministan sufuri Rotimi Amaechi, ya bayyanawa manema labarai bayan kammala taron na FEC cewa, ana sa ran layin dogon mai nisan kilomita 248 zai ratsa jahohin Kano da Katsina dake arewacin Najeriya, kuma zai zarce zuwa birnin Maradi a jamhuriyar Nijer dake makwabtaka da kasar ta yammacin Afrika.

An yi hasashen idan aikin ya kammala, layin dogon zai taimaka wajen jigilar danyen man fetur daga Nijer zuwa matatar man da ake ginawa a wani gari dake kan iyakar kasashen biyu, jaridar The Nation ta kasar ce ta wallafa rahoton a ranar Alhamis.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China