Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
NLC ta matsawa Najeriya lamba kan ta soke karin kudin wuta da man da ta yi
2020-09-17 19:30:00        cri

Gamayyar kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) ta baiwa gwamnatin Najeriya wa'adin kwanaki 14, kan ta soke karin kudin wuta da na man da ta yi, idan ba haka ba kuma, ma'aikata za su shiga yajin aiki.

Shugaban kungiyar ta NLC, Ayuba Wabba shi ne ya bayyana haka, yayin taron manema labarai da kungiyar ta kira jiya Laraba a Abuja, fadar mulkin kasar ta Najeriya. Yana mai cewa, 'yan Najeriya ba su ji dadin shawarar da gwamnati ta yanke ta karin kudin wuta da man ba. Watanni uku ke nan a jere Najeriya, kasa mai arzikin man fetur take kara kudin man, daga sama da naira 121, kwatankwacin kimanin dala 0.34 a watan Yuni zuwa naira 143 kan ko wace lita a watan Yuli, sai a watan Agusta inda ake sayar da man kan naira 150 kan ko wace lita da kuma naira 162 a watan Satumba.

A bangaren wutar lantarki kuwa, hukumomin Najeriya, sun amince karin kudin wutan zai fara aiki a faron watan Satumba da muke ciki, ko da yake, majalisar dokokin kasar ta dakatar da karin da a baya zai fara aiki tun a ranar 1 ga watan Yuli.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China