Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan sandan Najeriya sun tabbatar da kisan mutane 11 a harin da 'yan bindiga suka kai banki
2020-09-04 10:01:48        cri

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 11 sakamakon harin da 'yan bindiga suka kaddamar kan wani banki a shiyyar tsakiyar kasar.

Yan sanda sun kashe shida daga cikin 'yan fashin da ake zargi da yunkurin kai harin a lokacin da suka yi musayar wuta a kokarin da jami'an tsaron suka yi na hana gungun 'yan fashin samun damar shiga cikin bankin a garin Kagara dake jihar Neja a ranar Laraba, kamar yadda hukumomin 'yan sandan suka tabbatar.

Wasu mutanen biyar, da suka hada da 'dan sanda daya, da jami'in tsaro mai zaman kansa daya, da 'dan kato da gora daya, gami da fararen hula biyu sun rasa ransu, a lokacin musayar wuta da 'yan fashin, kamar yadda babban jami'in 'yan sandan jahar Adamu Usman, ya bayyana.

Usman ya fadawa 'yan jaridu cewa, 'yan fashin haye kan babura 4 sun yi yunkurin afkawa bankin dake yankin, amma tilas suka fasa sakamakon artabun da suka yi da 'yan sandan.

Ya kara da cewa, 'yan sandan suna ci gaba da bincike kan lamarin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China