![]() |
|
2020-09-04 20:10:15 cri |
Madam Hua ta ce, kasar Sin za ta ci gaba da sauke nauyin dake bisa wuyanta wajen biyan kudaden karo-karo da ya kamata ta baiwa MDD a matsayinta na kasa mai tasowa.
Rahotanni na cewa, a kwanakin nan, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya aikawa kasashe mambobin majalisar wasika, yana mai kira a gare su, da su biya kudaden ya kamata su biya a kan lokaci don taimakawa MDD kammala ayyukanta a wannan shekara. (Ibrahim Yaya)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China