![]() |
|
2020-09-22 19:49:56 cri |
Mista Wang ya bayyana hakan ne a Talatar nan, cewa shawarwarin da shugaba Xi ya gabatar, sun nuna ra'ayin kasar Sin na tsayawa kan tsarin kasa da kasa, a karkashin jagorancin MDD, da kare dokokin kasa da kasa, da rufa ma MDD baya, wajen ci gaba da taka muhimmiyar rawa a fannin daidaita al'amuran kasa da kasa, da aiwatar da manufar kasancewar bangarori daban daban masu fada a ji a duniyarmu, gami da kokarin shiga a dama da ita a aikin gyaran fuskar tsarin kula da harkokin kasa da kasa, da yunkurin kafa wata al'ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China