Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta harba na'urar binciken duniyar wata ta Chang'e-5
2020-09-20 16:50:48        cri
Mataimakin babban darekta mai kula da aikin bincike duniyar wata na kasar Sin, Yu Dengyun, ya bayyana a wajen taron zirga-zirgar kumbuna na kasar Sin na shekarar 2020, dake gudana a birnin Fuzhou na lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin cewa, ana gudanar da ayyukan binciken duniyar wata a kasar Sin lami lafiya, inda ake sa ran harba na'urar Chang'e-5 kafin karshen bana, wadda za ta sauka kan duniyar wata, da tattara wasu sinadarai dake can, gami da dawo da su duniyarmu.

A cewar mista Yu, wannan na'urar bincike, wato Chang'e-5, za ta kafa tarihi, musamman game da aikin zirga-zirgar kumbo na kasar Sin. Saboda za ta zama na'urar bincike ta kasar ta farko, da za ta tattaro wasu sinadarai a duniyar wata ita da kanta, kana za ta tashi daga duniyar wata, inda za ta sarrafa kanta don hada jikinta da wata na'ura ta daban dake shawagi a dab da duniyar, sa'an nan ta dawo duniyarmu tare da sinadaran da ta samu a duniyar watan.

Yu Dengyun ya ce, kasar Sin ta riga ta samu nasarori sosai a fannin binciken duniyar wata, inda ta riga ta harba wasu na'urorin bincike na Chang'e-1, zuwa na 4, gami da gwajin aikin dawowar Chang'e-5 duniyar mu. Da ma dai aikin binciken duniyar wata ya kunshi matakai 3, wato zagaya duniyar watan, da sauka a kan duniyar watan, gami da dawowa daga duniyar watan. Zuwa yanzu kasar Sin ta riga ta samu nasara wajen aiwatar da matakai guda 2 na farko. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China