Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Layin dogon Habasha zuwa Djibouti da Sin ta gina yana samun karin kudin shiga duk da annobar COVID-19
2020-09-19 15:59:13        cri

Jirgin kasan zamani wanda ya tashi daga Habasha zuwa kasar Djibouti ya samu karin sama da kashi 51 bisa 100 na kudaden shigarsa a watanni shidan farko na shekarar 2020 duk da kalubalolin da annobar COVID-19 ta haifar, kamfanin gudanar da jiragen kasar ce ta bayyana a ranar Juma'a.

Layin dogon mai tazarar kilomita 756, wanda ya fara aikin jigilar fasinjoji da kayayyaki tsakanin birnin Addis Ababa na kasar Habasha zuwa tashar ruwan kasar Djibouti a watan Janairun shekarar 2018, yana taka muhimmiyar rawa na biyan bukatun harkokin sufurin kasar Habasha da sauran yankuna masu makwabtanta dake zirin tekun Red Sea na kasar Djibouti.

Aikin layin dogon wanda kamfanonin kasar Sin biyu suka gudanar, ya kasance irinsa na farko a Afrika mai aiki da lantarki da ya ratsa kan iyakokin kasashe, ya samu gagarumin ci gaba tun bayan da ya fara aiki a watan Janairun shekarar 2018, kamar yadda kamfanin dake kula da jirgin kasan na Habasha zuwa Djibouti ya bayyana.

A yayin da yake ci gaba da fadada ayyukansa, a watan Agusta jirgin kasan ya fara aikin jigilar wasu nau'ikan hajoji, inda yake takon kayan marmari da na lambu daga kasar Habasha da ake sayar da su a kasashen Turai da sauran sassan duniya.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China