Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin a MDD ya yi kira da a inganta matakan yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi
2020-09-18 11:43:07        cri
Shugaban tawagar kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva Chen Xu, ya yi kira da sassan kasa da kasa, da su zage damtse wajen yayata manufofin cudanya da hadin gwiwar kasa da kasa, su kuma inganta kwazon su na tunkarar ayyukan ta'adanci da tsattsauran ra'ayi, don bunkasa, da kare 'yancin bil Adama.

Chen Xu wanda ya yi kiran, yayin taro ta kafar bidiyo game da yaki da ta'adanci, da sauya halayyar masu tsattsauran ra'ayi, wanda ya gudana jiya Alhamis, ya jaddada muhimmancin rawar da kasashen duniya za su iya takawa, wajen kafa al'ummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya, yana mai fatan sassan za su yi aiki tukuru, wajen aiwatar da kudurorin MDD masu nasaba da yaki da ta'addanci.

A cewar jami'in, yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa na Sin, ya sha fama da ayyukan ta'addanci da illar 'yan aware, da ayyukan masu tsattsauran ra'ayi. A baya, yankin ya fuskanci hare-hare, wadanda suka yi matukar barazana ga rayukan al'umma, da kyakkyanwan yanayin zamantakewarsu.

Chen Xu ya kara da cewa, mahukuntan Xinjiang sun mayar da batun kare rayuka da moriyar daukacin mazauna yankin gaban komai. Sun kuma aiwatar da matakai daban daban, na dakile yawaitar ayyukan ta'adanci, da sauya tunanin masu tsattsauran ra'ayi bisa doka. Kaza lika wadannan matakai sun haifar da manyan nasarori a fannin yaki da ta'addanci, da ba da kariya ga hakkokin bil Adama na dukkanin al'ummun yankin Xinjiang. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China