Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yang Jiechi: Kamata ya yi kungiyar BRICS ta kara ba da gudummawa a fannin wanzar da zaman lafiya da ci gaba
2020-09-18 10:47:42        cri
Mamba a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS Yang Jiechi, ya yi kira ga kasashe 5 mambobin kungiyar BRICS, da su kara ba da gudummawa a fannin wanzar da zaman lafiya, su zurfafa yarda da juna bisa matsayin koli. Yang wanda kuma shi ne daraktan ofishin lura da harkokin waje na kwamitin tsakiyar JKS, ya ce akwai bukatar kasashen na BRICS, su karfafa tattaunawa, su ba da babban tallafi ga ci gaba, da zaman lafiyar duniya.

Jami'in ya yi kiran ne yayin taro na 10, na manyan wakilan kasashen BRICS, game da batun tsaro wanda ya gudana ta kafar bidiyo. Ya ce yayin da ake tunkarar kalubalen cutar COVID-19, kasashen BRICS wato Brazil, da Rasha, da India, da Sin da Afrika ta kudu, sun nuna matukar jajircewa wajen yin hadin kai tare, don shawo kan wahalhalu masu tsanani da ake fuskanta.

Yang ya ce daukar matakai na kashin kai, da kariyar cinikayya, da nuna fin karfi, suna lahanta alakar kasashe, da tsaro a matakin kasa da kasa. Don haka ya zama wajibi kasashen kungiyar BRICS, su yi amfani da wannan gaba da MDD ke cika shekaru 75 da kafuwa, a matsayin damar kara rungumar manufofin ba da kariya ga ka'idojin MDD, da aiki tare wajen yayata manufar BRICS, ta wanzar da cudanyar dukkanin sassa yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China