Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai fargabar BH za ta dauki mayaka daga sansanin 'yan gudun hijira
2020-08-23 16:37:43        cri

Gwamnan jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya Umaru Zulum, ya yi gargadin cewa, akwai fargabar mayakan Boko Haram za su iya neman cimma matsaya don daukar mayaka daga sansanin 'yan gudun hijira.

Lamarin abin fargaba ne. Idan mazauna sansanonin suka gagara samun abubuwan da suke bukata, musamman samun damar sake komawa garuruwansu domin ci gaba da yin noma, mai yiwuwa Boko Haram ta tilasta musu shiga kungiyar, in ji gwamnan.

Da yake jawabi ga 'yan jarida a Maiduguri, babban birnin jihar ya ce, idan ba a dauki matakai ba, akwai yiwuwar a tilastawa mazauna sansanonin 'yan gudun hijirar shiga kungiyar.

Gwamnan ya ce, ko da yake, ana samun ingantuwar al'amurran tsaro a jihar, amma har yanzu akwai manyan kalubalolin kasancewar har yanzu 'yan ta'adda suna samun wuraren fakewa a yankunan jihar.

Game da yadda za a kawo karshen yaki da 'yan ta'addan, musamman mayakan Boko Haram, gwamnan ya ce, ya kamata a samu kyakkyawar fahimta tsakanin sojoji da fararen hula, idan hakan ta samu, ana sa ran sojojin za su yi bakin kokarinsu wajen tabbatar da ganin mutanen sun sake komawa garuruwansu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China