Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin: Hada kai shi babban makami na dakile COVID-19
2020-08-13 10:34:33        cri

A jiya Laraba zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya gabatar da wani jawabi a yayin taron muhawara na manyan jami'ai kan huldar annoba da zaman lafiya na kwamitin sulhun majalisar, inda ya jaddada cewa, gudanar da hada kai da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, shi ne makami mai karfi na dakile cutar numfashi ta COVID-19, ganin cewa, kasashen dake fama da tashin hankali sun fi shan wahala yayin da suke kokarin kandagarkin annobar, a don haka ya dace a samar musu da tallafi, ta yadda za a cimma burin ganin bayan annobar da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Zhang Jun ya yi nuni da cewa, tun bayan barkewar annobar COVID-19, kasar Sin tana himma da kwazo domin gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da kokarin samar da tallafi ga kasashen da suke bukata gwargwadon karfinta. A kwanakin baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron kolin musamman na Sin da Afirka da aka kira domin dakile annobar, taron da ya nuna anniyar sassan biyu ta ganin bayan annobar. Yanzu kasar Sin ta tsai da kuduri cewa, za ta soke basusukan da ya kamata wasu kasashen Afirka su biya ta kafin karshen shekarar 2020 da muke ciki, kuma idan ta yi nasarar hada allurar rigakafin cutar COVID-19, to jama'a a fadin duniya ne za su amfana da ita, domin taimakawa kasashe masu tasowa, kana kasar Sin za ta ci gaba da samar da kayayyakin kiwon lafiya ga kasashen da annobar ta fi kamari, da raba musu fasahohinta na jinyar cutar, hakazalika, kasar Sin za ta ci gaba da tura tawagogin ma'aikatan lafiya zuwa kasashen domin dakile annobar da ma jinyar marasa lafiya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China