Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilan kasashe daban-daban suna goyon bayan kasar Sin kan batun yankin Hong Kong da jihar Xinjiang
2020-09-16 13:46:13        cri

Jiya Talata, an gudanar da babbar muhawara kan rahoton manyan jami'ann musamman a fannin hakkin Bil Adama karo na 45, na majalissa mai kula da harkokin hakkin Bil Adam na MDD, inda wakilan kasashe daban-daban suka nuna goyon baya ga matakan da Sin take dauka, kan batun yankin Hong Kong da jihar Xinjiang.

Wakilin Burundi ya ce, kasar sa na maraba da dokar tsaron kasar Sin dake da alaka da yankin Hong Kong da Sin ta tsayar. A ganinta, dokar za ta ba da tabbaci ga tsarin "kasa daya tsarin mulki iri biyu", da ma taimakawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali da zaman wadata a yankin a cikin dogon lokaci, da ma tabbatar da harkokin hakkin Bil Adama a fannoni daban-daban.

Ban da wannan kuma, wakilin ya yabawa matakin da Sin take dauka na yakar ta'addanci da tsattsauran ra'ayi a jihar ta Xinjiang. Matakin ya kawar da tushen haifar da wadannan munanan abubuwa. Kaza lika, gwamnatin Burundi ta yabawa ci gaban da Sin take samu a fannin yakar cutar COVID-19, da ma nuna godiya ga taimakon da gwamnatin kasar Sin ke baiwa kasar ba tare da wani sharadi ba.

A nasa bangare, wakilin Habasha ya nuna cewa, harkokin yankin Hong Kong harkokin cikin gidan kasar Sin ne, kuma kasar na tsayawa tsayin daka kan goyon bayan aiwatar da tsarin "kasa daya amma tsarin mulki iri biyu" a yankin, tana kuma adawa da mai da batun kare hakkin Bil Adama matsayin batun siyasa, da ma fakewa da wannan batu don tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China