Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakiliyar MDD ta ankarar da duniya kan yadda ake kaiwa makarantu hare-hare
2020-09-11 11:20:35        cri
Wakiliyar babban sakataren MDD ta musamman kan harkokin yara da tashe-tashen hankula Virginia Gamba, ta ankarar da duniya kan yadda a 'yan shekarun nan, masu dauke da makamai ke ci gaba da kaiwa malamai da makarantu hare-hare ba gaira ba dalili

Jami'ar wadda ta bayyana haka, yayin wani taron muhawara da kwamitin sulhun MDD ya shirya kan yadda ake kaiwa makarantu hare-hare, ta kuma nuna damuwa kan yadda lamarin ya yi Kamari, musamman a yakin Sahel, inda ake kaiwa makaranatun mata hari.

Ta ce, a cikin shekaru da suka gabata ma, an yiwa wasu malamai barazana tare da kashe su a kasar Mali, baya ga lalata cibiyoyin Ilimi da kuma kona kayayyakin more rayuwa, matakin da ya sabbaba rufe makarantu sama da 1,260, kafin ma bullar cutar numfashi ta COVID-19.

Ta ce, lamarin ya ki Kamari a shekarar da ta gabata, inda aka kaiwa makarantu da malamai hare-hare a kasar Burkian-Faso, ciki har da kona makarantu da yin garkuwa da malamai, matsalar da ta tilasta rufe makarantu kimanin 2,500, da hana dubban daruruwan yara samun ilimi.

A don haka, Gamba ta yi kira ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki, da su kare yara da malamai, a kuma mutunta kayayyakin more rayuwa na fararen hula. Ta kuma tunatar da gwamnatoci cewa, hakkinsu ne su kare harkar Ilimi, ko da a lokutan yaki ne da kuma annoba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China