Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
GDPn kasar Sin zai bunkasa matuka a rubu'i na uku na bana
2020-09-15 19:02:06        cri

Hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta bayyana cewa, hasashe na nuna cewa, tattalin arzikin kasar zai bunkasa cikin sauri a rubu'i na uku na shekarar bana, idan har karfin farfadowarsa ya ci gaba kamar yadda yake a watan Satumba.

Mai magana da yawun hukumar Fu Linghui, shi ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da aka shirya Talatar nan, yana mai cewa, an samu ingantuwar kayayyakin da masana'antu ke samarwa gami da ayyukan hidima, a rubu'i na uku, idan aka kwatanta da rubu'i na biyu na bana.

Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, ayyukan masana'antun kasar, muhimmin alkaluman dake nuna karfin tattalin arziki, ya karu zuwa kaso 5.6 cikin 100, kan na watan Agustan shekarar da ta gabata, karuwar kaso 4.8 a watan Yuli.

Haka kuma GDPn kasar ta Sin ya karu da kaso 3.2 a rubu'i na biyu na shekara bisa makamancin lokaci na bara, amma a rubu'in farko ya ragu da kaso 6.8 cikin 100.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China