Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kimar Sin a duniya tana kara kyautatuwa
2020-09-15 18:47:30        cri

Yau a nan birnin Beijing, cibiyar nazarin harkokin kasar Sin da na kasashen duniya a zamanin yanzu ta hukumar wallafa rahotannin harsunan waje ta kasar Sin ta fitar da wani rahoto mai taken "rahoton bincike kan kimar kasar Sin a fadin duniya na shekarar 2019", inda aka bayyana cewa, kimar kasar Sin a idon al'ummun kasa da kasa tana kara kyautatuwa, har ana sa ran kasar Sin za ta kara taka rawa a bangaren ci gaban kasashen duniya.

Cibiyar nazarin harkokin kasar Sin da na kasashen duniya a zamanin yanzu ta hukumar wallafa rahotannin harsunan waje ta kasar Sin da kamfanin yin bincike na Kantar sun fitar da rahoton ne cikin hadin gwiwa, bayan da suka gudanar da bincike kan mutane dubu 11 dake kasashe 22.

Rahoton binciken ya nuna cewa, a shekarar 2019 da ta gabata, kasar Sin tana kara samun karbuwa a wajen mutanen da aka yiwa binciken a kasashen ketare, inda sama da kaso 60 bisa dari dake cikinsu suna ganin cewa, kimar kasar Sin a idon al'ummun kasa da kasa ta ci gaba da kyautata a cikin shekaru 70 da suka gabata, kana sun jinjinawa sakamakon da kasar Sin ta samu a cikin wadannan shekarun.

Ban da haka, an lura cewa, wadanda aka yiwa binciken dake ketare sun fi nuna sha'awa kan ci gaban kasar Sin a fuskokin tattalin arziki da kimiyya da fasaha, inda kaso 68 bisa dari daga cikinsu sun dauka cewa, kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na kasar Sin yana da karfi, musamman ma wajen gina layin dogo mai saurin tafiya.

Hakazalika, kaso 60 bisa dari sun amince da ma'anar tunanin gina kyakkyawar makomar bil Adam ga daukacin al'ummar duniya da kuma tafiyar da harkokin kasa da kasa, kana shawarar ziri daya da hanya daya muradun kasar Sin ne da ya fi samun karbuwa a wajen al'ummun kasashen ketare.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China